Shugaba Tinubu ya sauka da zafinsa, inda ya bayyana cewa "Ina jiran cikakken rahoto kan hatsarin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Shugaba Tinubu ya sauka da zafinsa, inda ya bayyana cewa "Ina jiran cikakken rahoto kan hatsarin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jajantawa ga fasinjojin jirgin kasa na Abuja–Kaduna da ya yi hatsari a ranar Talata a kan hanyar Kaduna, inda ya bayyana cewa yana jiran cikakken bayani domin ɗaukar mataki cikin gaggawa da kuma samar da tallafi ga duk wanda lamarin ya shafa.

A halin da ake ciki, Manajan Darakta na Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Mista Kayode Opeifa, ya É—auki cikakkiyar alhakin hatsarin da ya faru.

Haka kuma, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya yi kira da a sake gina amincewar jama’a kan ababen more rayuwar sufuri a Najeriya, bayan wannan hatsari da ya faru.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)